Allardyce ya zama sabon kocin Sunderland

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A watan Yuni, Allardyce ya raba gari da West Ham

Sunderland ta nada Sam Allardyce a matsayin sabon kocin kungiyar, inda ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu.

A ranar Lahadi, Dick Advocaat ya ajiye mukaminsa bayan da kungiyar ta buga wasanni takwas ba tare da ta samu nasara ba.

Allardyce mai shekaru 60, bai da aiki tun da ya bar West Ham a karshen kakar wasan da ta wuce.

"Aiki ne mai cike da kalubale. Amma ina sa ran zai taimakawa kungiyar," Allardyce.

Allardyce ya taba murza leda a Sunderland daga shekarar 1980 zuwa 1981.

Ya zama mutum na farko da ya jagoranci Sunderland da kuma Newcastle da suke hammaya tare.