Muna tattaunawa da Sunderland - Allardyce

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Sam Allardyce na tattaunawa da Sunderland game da shugabancin kulob din.

Sunderland na tattaunawa da Sam Allardyce a filin wasan Stadium of light, game da cike gurbin shugabancin kulob din.

Tsohon kocin ya bar kulob din ranar Lahadin da ya gabata, sakamakon koma baya da kulob din ta yi a teburin gasar kofin Turai da shan kashi a duk wasannin guda takwas da suka buga.

Allardyce mai shekaru 60 yana zam,an kashe wando ne tun lokacin da ya bar West Ham a karshen kakar wasa a bara.

Ya shugabancin Bolton da Blackburn a baya, ya kuma murza leda a matsayin dan kwallon Sunderland daga shekarar 1980 zuwa 1981, inda kuma ya yi fice a wasan da suka yi da Newcastle a shekarar 2007 da 2008.

Bayan tafiyar Advocaat, Allardyce shi ne na takwas da zai jagoranci Sunderland a cikin shekaru bakwai, kuma wanda Advocaat ya maye gurbin sa, Gus Poyet a baya, ya nuna goyon bayan sa ga daukar Allardyce.

"Ya san abun da aikin ya tanada tun a baya, yana kuma da masaniya a kan tsarin gasar kofin Turai " In ji Gus Poyet.