"Hayatou nada koshin lafiyar jan ragamar Fifa"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hayatou ya fara jagorantar CAF a shekarar 1988

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta ce Issa Hayatou yana da koshin lafiya da zai iya aikin riko na shugaban Fifa, duk da rashin lafiya da yake fama da yi.

Hayatou dan kasar Kamaru, zai je Zurich a ranar Talata domin fara aiki a Fifa, duk da cutar koda da yake fama da ita wanda yake bukatar kulawa daga wajen likitoci a kai - a kai.

CAF ta ce Hayatou bai taba fashin aiki ba tun lokacin da aka zabe shi domin jan ragamar hukumar kwallon kafa ta Afirka.

Hukumar ta ci gaba da cewa ba wani boyayyen abu ba ne cewar Hayatou yana fama da ciwon koda, saboda yana ganin likita yadda ya kamata.

Hayatou mai shekaru 69, zai karbi aikin shugabatar Fifa na rikon kwarya ne, bayan da aka dakatar da Sepp Blatter daga aiki tsawon kwanaki 90.

Hayatou ya fara jan ragamar hukumar kwallon kafa ta Afirka a shekarar 1988, zai kuma karbi aikin shugabatar Fifa na riko a mako mai zuwa.