Platini ya kalubalanci dakatar da shi daga Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwamitin da'a na Fifa ne ya dakatar da Platini daga aiki tsawon kwanaki 90

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini ya kalubalanci dakatar da shi da aka yi daga Fifa, bayan da ake yin bincike kan cin hanci.

An dakatar da Platini mai shekaru 60 tare da shugaban Fifa, Sepp Blatter da sakatare janar na hukumar Jerome Valcke daga aiki tsawon kwanaki 90, kuma dukkansu sun karyata aikata ba dai-dai ba.

Platini mataimakin shugaban hukumar Fifa, yana daga cikin masu yin takarar kujerar shugabancin hukumar domin maye gurbin Sepp Blatter.

Hukumar kwallon kafar Faransa na son kotun daukaka karar wasanni ta shiga cikin batun, domin bai wa Platini damar yin takara a zaben da za a yi a cikin watan Fabrairu.

Kwamitin da'a na hukumar Fifa ne ya dakatar da jami'an uku, bayan da Switzerland ta fara bincikar Sepp Blatter a watan Satumba kan aikata ba dai-dai ba a Fifa.