Ya ci ace an dauki mataki kan raunata Shaw - Collina

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption PSV ce ta doke Manchester United da ci 2-1 a karawar

Ya kamata ace an hukunta Hector Moreno a ketar da ya yi wa dan kwallon Manchester United, Luke Shaw in ji tsohon alkalin wasa Pierluigi Collina.

Alkalin wasa Nicola Rizzoli bai dauki mataki kan ketar da dan wasan PSV Eindhoven, Moreno ya yi wa Shaw a gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a watan jiya ba.

Collina ya ce mun sha tunatar da alkalan wasa da su kula da kuma maida hankali kan hukunta 'yan wasa masu irin wannan dabi'ar.

Ya kuma ce babu wanda ya tsinkayi abinda ya faru har da su kansu 'yan wasan da suke buga karawar a lokacin.

Collina dan kasar Italiya wanda ya yi ritaya daga alkalancin wasa a shekarar 2005, ya ce abinda yake daure wa mutane kai kenan a inda aka ci gaba da taka leda ba tare da an tsaida wasan ba nan take.