Siasia ya gayyaci 'yan wasa 30 sansanin horo

Hakkin mallakar hoto Thenff
Image caption Senegal ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta matasa 'yan kasa da shekaru 23

Samson Siasia ya gayyaci 'yan wasa 30 masu shekaru kasa da 23 zuwa sansanin horo a Abuja Nigeria.

Cikin 'yan wasan ne zai fitar da wadanda za su wakilci Nigeria a gasar cin kofin nahiyar Afika ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 da Senegal za ta karbi bakunci a watan gobe.

Siasia ya gayyato 'yan wasa 19 da suke buga gasar Firimar Nigeria da kuma karin 11 daga wasu kungiyoyin kwallon kafa da suke wasa a Nigeria.

Haka kuma yawan cin 'yan kwallon da ya gayyato suna cikin wadanda suka sami mataki na uku a gasar wasannin Afirka da aka kammala a Congo Brazzaville.

Kocin ya umarci 'yan kwallon da ya gayyata da su halarci otal din Serob Legacy dake Abuja ranar Lahadi 11 ga watan Oktoba domin fara atisaye a ranar Litinin 12 ga watan na Oktoban.

Ga sunayen 'yan was an da aka gayyata:

 1. Daniel Emmanuel (Enugu Rangers)
 2. Yusuf Mohammed (Kano Pillars)
 3. Erhun Obanor (Abia Warriors)
 4. Segun Oduduwa (Nath Boys)
 5. Sincere Seth (Rhapsody FC)
 6. Ndifreke Effiong (Abia Warriors)
 7. Chima Akas (Sharks FC)
 8. Usman Mohammed (FC Taraba)
 9. Godspower Effiong (Kano Pillars)
 10. Daniel Etor (Enyimba FC)
 11. Etebo Oghenekaro (Warri Wolves)
 12. Tiongoli Tonbara (Bayelsa United)
 13. Wanbe Godwin (Enugu Rangers)
 14. Austine Oladapo (FC IfeanyiUbah)
 15. Semiu Laidi (Warri Wolves)
 16. Kingsley Sokari (Enyimba FC)
 17. Christian Pyagbara (Sharks FC)
 18. Iroha Ebuka (Diamond FC)
 19. Qudus Suleiman (36 Lions)
 20. Yusuf Lawal (36 Lions)
 21. Adebayo Ajadi (36 Lions)
 22. Israel Emmanuel (Akwa United)
 23. Akinola Johnson (Freestan FC)
 24. Tochukwu Nnorom (Enugu Rangers)
 25. Chukwudi Esoze (Kwara United)
 26. Stanley Dimgba (Warri Wolves)
 27. Lucky Jimoh (36 Lions)
 28. Philip Johnson Effiong (Abia Comets)
 29. Ajabor Sunday(Freestan FC)
 30. Charles Chukwudi (Plateau United)