Euro 2016: Italiya ta samu tikitin zuwa Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Italiya ta ci dukkan wasanninta da ta buga na cikin rukuni

Kasar Italiya ta samu tikitin buga gasar cin kofin nahiyar Turai da za ayi a Faransa a 2016, bayan da ta doke Azerbaijan da ci 3-1 a fafatawar da suka yi ranar Asabar a Baku.

Italiya ce ta fara zura kwallo ta hannun Eder dan kwallon Sampdoria, nan da nan Azerbaijan ta farke kwallo ta hannun Dmitri Nazarov.

El Shaarawy ne ya kara ci wa Italiya kwallo ta biyu sannan kuma dan wasan Manchester United, Matteo Darmian ya kara ta uku a raga.

Azerbaijan ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Badavi Huseynov jan kati a wasan.

Wannan shi ne karo na shida da Italiya ta kai wasan gasar cin kofin nahiyar Turai a jere, wacce ta kasa zuwa gasar da Sweden ta karbi bakunci a shekarar 1992.

Italiya ce ta jagoranci rukunin na takwas da maki 21, sai Norway da Croatia da suke neman gurbin mataki na biyu domin samun damar shiga gasar da za a yi a badin.

Norway za ta ziyarci Italiya a wasan karshe na cikin rukuni, yayin da za a kara tsakanin Croatia da Malta a ranar Talata.

Sakamakon wasannin da aka buga:

  • Iceland 2 - 2 Latvia
  • Kazakhstan 1 - 2 Netherlands
  • Czech Rep. 0 - 2 Turkey
  • Andorra 1 - 4 Belgium
  • Bos-Herze 2 - 0 Wales
  • Israel 1 - 2 Cyprus
  • Azerbaijan 1 - 3 Italy
  • Norway 2 - 0 Malta
  • Croatia 3 - 0 Bulgaria