Mai Caji da Horo sun kara takawa a dambe

Image caption Kai kora suka yi a wannan takawar, Ashiru Horo ya ji rauni a hannun hagunsa

An sake sa zare tsakanin Ashiru Horo Sarkin dambe daga Arewa da Mai Caji daga Kudu da sanyin safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Tun kafin su fara wasan makadin 'yan dambe Autan Mai Turare ya wasa Ashiru Horo, shi kuwa Mamuda Kanoma ya koda Mai Caji.

Nan da nan suka shiga filin wasa, sai dai abinka da tsautsayi takawar farko Mai Caji ya kai duka shi kuwa Horo ya kare da hannun hadu kuma hakan ya sa ya ji rauni ba a ci gaba da wasan ba.

Tun farko dai an fara dambatawa ne tsakanin Shagon Alhazai daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada kuma turmi biyu suka yi babu kisa aka raba wasan.

Shi kuwa Amwa Shagon Shagon Mada daga Kudu doke Fijot ya yi daga Arewa a turmin farko, aka tashi wasa babu kisa tsakanin Sojan Kyallu daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu.

Shi kuwa Shagon Shukurana daga Arewa doke Dogon Kurari ya yi daga Kudu, kuma sai da aka dauki minti bakwai kafin Dogon Kurari ya farfado daga sumar da shi da aka yi.

Fijot daga bangaren Arewa ya kara dambatawa a karo na biyu da Garkuwan Mai Caji daga Arewa kuma turmi biyu suka taka aka raba fafatawar.