Bai kamata FA ta marawa Platini baya ba - Robertson

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Platini na fatan maye gurbin Sepp Blatter a zaben da za a yi a watan Fabrairu

Tsohon ministan wasanni Sir Hugh Robertson ya ce bai kamata hukumar kwallon kafa ta Turai ta ci gaba da marawa Michel Platini baya kan takarar kujerar shugabantar Fifa ba.

Platini wanda Fifa ta dakatar, shi ne kuma wanda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ke fatan zai maye gurbin Sepp Blatter a matsayin sabon shugaban hukumar a zaben da za a yi a cikin watan Fabrairu.

Robertson ya ce ya kamata Fifa ta samu sabon shugaba wanda baya cikin wadanda suka jagoranci hukumar.

Kwamitin da'a na Fifa ne ya dakatar da Sepp Blatter da sakatare janar na hukumar Jerome Valcke da kuma Platini kan zargin cin hanci da ake bincikensu.

Dukkansu sun karyata zargin da ake yi musu, kuma Blatter da Platini sun kai kara kan dakatar da su da aka yi daga shiga harkokin Fifa kwanaki 90.