Kano Pillars ta ci Sunshine Stars 2-1

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Sauran wasanni biyar a kammala gasar firimiyar bana

Kano Pillars ta doke Sunshine Stars da ci 2-1 a gasar cin kofin firimiyar Nigeria wasan mako na 33 da suka kara a jihar Kano ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Enyimba ma kwallaye 2-1 ta doke Shooting Stars, sai Sharks da ta ci Wikki Tourists 2-0, yayin da Nasarawa United ma ta doke Bayelsa 2-1 a Yenagoah.

Taraba FC kuwa daya mai ban haushi ta ci Heartland, ita ma Giwa FC 1-0 ta doke Dolphins, sai kuma fafatawa tsakanin Rangers da Warri Wolves da suka tashi kunnen doki 1-1.

Ifeanyiubah kuwa ta samu maki uku da kwallaye uku bayan da El-Kanemi Warriors ba ta halarci karawar ba.

Ga sakamakon wasan mako na 33 da aka buga:

  • Giwa FC 1-0 Dolphins
  • Sharks 2-0 Wikki
  • FC Taraba 1-0 Heartland
  • Enyimba 2-1 Shooting Stars
  • Bayelsa Utd 1-2 Nasarawa Utd
  • Lobi Stars 2-1 Kwara Utd
  • Akwa Utd 1-0 Abia Warriors
  • Kano Pillars 2-1 Sunshine Stars
  • Rangers 1-1 Wolves