U-20 Mata: Nigeria za ta fafata da Afirka ta Kudu

Image caption A shekara mai zuwa za a buga gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20

Tawagar kwallon kafar mata ta matasa 'yan kasa da shekaru 20 ta Nigeria za ta kara da ta Afirka ta Kudu a wasan karshe na neman tikitin shiga gasar kofin duniya ta mata da za a yi a badi.

Nigeria ta kai wannan matakin ne bayan da ta doke Jamhuriyar Congo da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a Abuja, kuma Nigeria ta ci kwallaye 4-1 kenan a karawa biyu da suka yi.

Ita kuwa Afirka ta Kudu doke Zambia ta yi da ci 3-1, a wasan farko da suka kara a Zambiya tashi suka yi 0-0.

Nigeria ce za ta fara karbar bakincin Afirka ta Kudu a Abuja ranar Asabar 24 ga watan Oktoba, sannan su buga wasa na biyu a Johannesburg makonni biyu tsakani.

Daya gurbin da zai wakilci Afirka a gasar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 20 ta duniya, za a yi ne tsakanin Ghana da Habasha.