2018 Wold Cup: Wasannin karshe na neman gurbi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe biyar ne suke wakiltar Afirka a gasar cin kofin duniya

Sauran wasannin share fage 10 da za a yi a ranar Talata, domin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2018 da Afirka za ta fitar da wakilanta.

A ranar Talata ne za a kammala wasannin share fagen shiga jadawalin neman gurbin kasashe biyar da za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniyar da Rasha za ta karbi bakunci.

Haka kuma a cikin watan gobe ne za a kara a wasannin gida da waje tsakanin kasahen da za su fafata domin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniyar.

Ga yadda za a karasa wasanni share fagen:

 • Niger ko Somalia (0-2) vs Kamaru
 • Swaziland ko Djibouti (6-0) vs Nigeria
 • Mauritania ko South Sudan (1-1) vs Tunisia
 • Botswanko Eritrea (2-0) vs Mali
 • Namibia ko The Gambia (1-1) vs Guinea
 • Burundi ko Seychelles (1-0) vs DR Congo
 • Chad ko Sierra Leone (1-0) vs Egypt
 • Guinea-Bissau ko Liberia (1-1) vs Ivory Coast
 • Lesotho ko Comoros (0-0) vs Ghana
 • Madagascarko CAR (3-0) vs Senegal

Ga kuma sauran wasannin gaba na share fagen:

 • Ethiopia v Congo
 • Morocco v Equatorial Guinea
 • Kenya v Cape Verde
 • Mozambique v Gabon
 • Tanzania v Algeria
 • Benin v Burkina Faso
 • Sudan v Zambia
 • Togo v Uganda
 • Libya v Rwanda
 • Angola v South Africa

A cikin watan Nuwamba za a fitar da rukuni biyar da zai kunshi kasashe hudu da za su fafata a tsakaninsu, kuma zakara daga kowanne rukuni ya wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya a 2018.