Kotu ta ce a saki 'ya'yan Hosni Mubarak

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alaa da Gamal Mubarak na fuskantar tuhuma iri-iri

Wata kotu a Masar ta bada umurnin sakin 'ya'yan habararren shugaban kasar, Hosni Mubarak su biyu maza.

'Ya'yan tsohon shugaban, suna zaman kurkuku ne bayan da aka yanke musu hukuncin daurin shekaru uku bisa zargin cin hanci da karbar rashawa.

Kotun ta bayar da umunin a saki Alaa da Gamal Mubarak ne, saboda tayi la'akari da cewar tun a shekarar 2011 ake tsare da su.

Har yanzu suna jiran a yanke musu hukunci a kan wata shari'ar da ake zarginsu da wawure dukiyar al'umma.

Su na kuma fuskantar shari'a a kan wasu zarge-zargen masu nasaba da cuwa-cuwa a hukumar kula da hannun jari ta Masar.