Babu cuwa-cuwa tsakanin Blatter da Platini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Fabrairu za a yi zaben shugaban hukumar Fifa

BBC ta faminci cewar babu wata takardar shaidar cewa Fifa ta bai wa Michel Platini kudade sama da dala miliyan daya da dubu dari uku.

Kwamitin da'a na hukumar Fifa ne yake binciken biyan kudi da aka yi wa Platini shekaru tara da suka wuce, saboda wani aiki da ya yi wa Sepp Blatter.

An dakatar da Platini shugaban hukumar kwallon kafar Turai da kuma Blatter daga aiki kwanaki 90, ana kuma cigaba da bincikensu kan zargin cin hanci.

A watan Satumba ne Switzerland ta fara binciken Blatter bisa zargin cin hanci a hukumar kwallon kafa ta Fifa.