Samun tikitin gasar Turai ya fi daukar kofin zakaru

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da Wales ta buga wata babbar gasar kwallon kafa tun a shekarar 1958.

Gareth Bale ya ce samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Wales ta yi ya fi daukar kofin zakarun Turai.

Wales ta samu kaiwa gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a badi, duk da doke ta 2-0 da Bosnia-Herzegovina ta yi a ranar Asabar.

Kuma doke ta da aka yi a ranar Asabar ya kawo karshen lashe wasanni 11 da Wales ta yi a jere.

Bale ya ce samun tikitin shiga gasar Turai da suka yi ya fi komai mahimmaci.

Bale mai taka leda a Real Madrid ya ci wa Wales kwallaye 6 ya kuma bayar da biyu da aka zura a raga a wasannin neman gurbin shiga gasar da suka buga.

Rabon da Wales ta halarci wata babbar gasar kwallon kafa tun wacce ta buga a gasar cin kofin duniya a shekarar 1958.