Roger Federer ya sha mamaki a Shanghai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer ya fice daga gasar Shanghai Masters

Dan wasan tennis na uku a duniya, Roger Federer, ya fice daga gasar Shanghai Masters bayan da ya sha kashi a hannun Albert Ramos-Vinolas.

Wannan ne dai wasa na farko da Federer, wanda ke kare kambunsa, ya buga tun bayan da Novak Djokovic ya yi nasara a kan shi a wasan karshe na gasar US Open.

Babbar gasa daya kacal Ramos-Vinolas, wanda shi ne na 70 a duniya, ya lashe a kakar wasanni uku da suka gabata, kuma bai taba yin nasara a kan 'yan wasa goman da ke kan gaba ba a duniya.

Nan gaba Ramos-Vinolas, wanda dan kasar Spain ne, zai fuskanci Jo-Wilfried Tsonga ko Victor Estrella Burgos.