Gasar 2018: Nijar ta kai mataki na gaba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Nijar, Moussa Maazou, ne ya ci kwallaye biyu a zagayen farko

Nijar da Chadi na cikin kasashen da suka samu kaiwa zagaye na gaba na wasannin neman gurbi a Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ta 2018.

Sauran kasashen da suka kai matakin na gaba su ne Burundi, da Madagascar, da Namibia.

Jamhuriyar ta Nijar ta samu kaiwa wannan matakin ne bayan ta lallasa Somalia da ci hudu ba ko daya ranar Talata.

A ranar Juma'a Nijar din ta casa Somalia da ci biyu ba ko daya a zagaye na farko na wasan nasu.

Da hakan dai, jimillar kwallayen da Nijar din ta ci sun kama shida ke nan, kuma a mataki na gaba za ta kara da Kamaru.