Jami'an UEFA za su shawarta kan Platini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Michel Platini na sa ran maye gurbin shugaban FIFA Sepp Blatter badi

Ana sa ran ranar Alhamis shugabannin hukumomin kwallon kafa na Turai za su yanke shawara a kan ko za su ci gaba da goyon bayan takarar Michel Platini ta neman shugabancin FIFA ko kuma su juya baya ga mutumin da ya yi shekaru takwas yana shugabantar su.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mai yiwuwa manyan jami'an kwallon na Turai su nemi a dage zaben shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya daga 26 ga watan Fabrairun badi, lamarin da ka iya bai wa Platini isasshiyar dama ya kare kansa. Sai dai yin hakan zai sa a yi korafin nuna son-kai.

In ba haka kuwa, to shugabannin na hukumomin kwallon kafa na Turai na da makwanni biyu ne kacal don su nemo wanda zai maye gurbin Platini kafin cikar wa'adin yin rajistar sha'awar tsayawa takarar shugabancin FIFA wanda ke cika ranar 26 ga watan Oktoba.

A shekarar da ta gabata dai Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta zuba wa sarautar Allah ido ne yayin da hukumar ta FIFA ke fuskantar badakala mafi muni a shekaru 111 na kafuwarta.