Golden Eaglets sun dira a Chile

Golden Eaglets Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Tawagar ta Golden Eaglets ta tashi zuwa Santiago ne bayan wasannin sada zumunta

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Golden Eaglets ta sauka a Santiago, babban birnin kasar Chile, inda za ta kare kambunta a Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya ta 'yan kasa da shekaru 17.

Ranar Asabar 17 ga wannan wata na Oktoba za a fara gasar, wadda za a kammala ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba.

Najeriya ce dai ta lashe gasar wacce aka yi shekaru biyu da suka gabata a Hadaddiyar Daular Larabawa; da ita ne kuma tawagar ta Golden Eaglets ta kafa tarihi inda ta lashe gasar sau hudu.

Kocin tawagar, Emmanuel Amuneke, ya ce: "Mun zo nan ne don kare kambunmu. Mun zo da sababbin 'yan wasa wadanda ke da burin kafa nasu tarihin, kuma muna dokin buga wasanmu na farko da Amurka, wanda wasa ne mai matukar muhimmanci".

Karin bayani