FIFA ta dakatar da tsohon jami'in SAFA

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta dakatar da wani tsohon jami'in Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta Kudu, SAFA, daga harkar kwallon kafa har tsawon shekaru shida.

Kwamitin da'a na hukumar ta FIFA ne ya yanke wannan hukuncin a kan Lindile Kika.

FIFA ba ta bayar da wani bayani ba game da dalilin dakatar da jami'in ba, sai dai kawai ta ce abin "na da alaka da wadansu wasannin sada zumunta da aka buga a Afirka ta Kudu a shekarar 2010".

Kika ya musanta zargin cewa yana da hannu a wata badakalar sayar da wasanni tun daga 2010.

Yana cikin wadansu manyan jami'an SAFA biyar da aka bai wa hutu na musamman a watan Disamban 2012 bayan wani rahoton FIFA a kan sayar da wasanni.

Kuma ko da yake an mayar da su mukamansu a watan Janairun 2013, ba a wanke su daga aikata laifi ba.

Karin bayani