Muna goyon bayan Platini - UEFA

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Michel Platini

Hukumomin kwallon kafa a kasashen Turai sun bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ta yanke hukunci a kan zarge zargen cin hanci da ake yi wa Michel Platini zuwa tsakiyar Nuwamba.

Platini shi ne ke shugabantar hukumar kula kwallon kafar Turai UEFA.

Kungiyoyin sun ce suna goyon bayan matakin da Mista Platini ya dauka na kare kansa, sai dai wakilin BBC a wajen wani taro da suka yi, ya ce akwai wasu daga cikin mambobin kungiyoyin da suke tunanin sauya Platinin.

An dakatar da Mista Platini ne daga mukamin mataimakin shugaban hukumar ta FIFA na kwani 90, saboda zargin ya karbi rashawar fiye da dala biliyan 2 daga shugaban hukumar FIFA da aka dakatar Sepp Blatter.