Ba na tsoron kashe kudi kan sayo dan wasa - Wenger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce kulob din ba ya tsoron kashe kudade a kasuwar sayar da 'yan wasa.

Wenger mai shekaru 60, ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki na shekara-shekara cewa kulob din ba shi da wata matsala ta kudi, bisa la'akari da kudin shigarsa a shekara £344.5m da kuma ribar £24.7m.

Dan wasa daya tal Arsenal ta saya a kakar wasannin bana, wato mai tsaron raga Petr Cech daga Chelsea.

"Ba ma tsoron kashe kudi, na san kowa ya sanni da haka, idan dan wasa ya cancanci mu saye shi, za mu kashe kudi akan sa", in ji Wenger.

Wenger ya sha suka daga wasu magoya bayan kulob din saboda ya ki sayo dan wasan gaba kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa, duk da ya san Danny Welbeck zai yi jinya har zuwa Kirsimeti.