Ina son in zama kocin Spain - Enrique

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Enrique ya haskaka a Barcelona

Kocin Barcelona, Luis Enrique ya ce yana sha'awar kasancewa kocin Spain idan Vicente del Bosque ya tafi.

Del Bosque mai shekaru 64, zai jagoranci Spain zuwa gasar cin kofin Turai sau uku a jere kuma kwangilarsa za ta kare ne bayan kamalla gasar a Spain.

Da aka tambaye shi ko yanason maye gurbin Del Bosque sai Enrique ya ce "Tabbas ina son aikin sosai."

Yarjejeniyar Enrique da Barcelona za ta kare ne a shekarar 2017.

Dan shekaru 45, ya buga wa Spain wasanni 62 daga shekarar 1991 zuwa 2002.

Ya kuma jagoranci Barcelona ta lashe kofuna uku a kakar wasan da ta wuce inda ta lashe kofin La Liga da na zakarun Turai da kuma na Copa del Rey.