Zan yi sauye-sauye a Fifa - Hayatou

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban riko na Fifa, Issa Hayatou ya ce akwai bukatar hukumar kwallon duniya ta maido da kimarta a idon duniya.

A ranar Alhamis ne, Hayatou ya isa shalkwatar Fifa a Zurich a karon farko tun da ya maye gurbin Sepp Blatter da aka dakatar.

A yanzu haka dai Fifa na gudanar da bincike a kan zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa kan manyan jami'anta.

"Lamarin babu dadi amma dai zamu mayar da hankali a sauye-sauyen da suka dace," in ji Hayatou.

A ranar 8 ga watan Oktoba ne, hukumar Fifa ta sanar da dakatar da shugabanta, Sepp Blatter da Sakatare Janar Jerome Valcke da kuma shugaban Uefa, Michel Platini na tsawon kwanaki 90.