Djokovic ya doke Murray a Shanghai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a buga wasan karshe na cin kofin Shanghai Master a ranar Lahadi

Novak Djokovic ya kai wasan karshe a gasar kwallon Tennis ta Shanghai Masters, bayan da ya doke Andy Murray da ci 6-1 da kuma 6-3.

'Yan wasan biyu sun kara ne a wasan daf da karshe domin lashe kofin Shanghai din.

Tun da suka fara wasan Djokovic ya fara doke Murray cikin sauki ba tare da matsi ba.

A wasa na biyu kuwa Murray ya dan tabuka, amma hakan bai hana a sake buge shi ba.

Daya wasan daf da karshen Jo-Wilfried Tsonga ne ya doke Rafael Nadal da ci 6-4 da 0-6 da kuma 7-5.

Da wannan sakamakon Jo-Wilfried Tsonga zai fafata a wasan karshe da Novak Djokovic a ranar Lahadi.