Wenger ya bukaci 'yan wasa su kara kaimi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal ce za ta karbi bakuncin Bayern Munich a Emirates

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya bukaci 'yan wasansa da su kara kaimi domin doke Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai da za su yi ranar Talata.

Wenger ya ce idan har suka samu nasara a kan Bayern hakan zai karfafa musu gwiwa da kuma tabbatar da cewar ba a fitar da su daga gasar da wuri ba.

Arsenal wacce take mataki na biyu a kan teburin Premier, ta yi rashin nasara a wasanni biyu da ta buga da Dinamo Zagreb da kuma Olympiakos a gasar ta zakarun Turai.

A tarihi Gunners ta yi rashin nasara a hannun Bayern a wasanni biyu a gida, yayin da ta je Jamus ta ci wasa daya ta kuma yi kunnen doki da su a karawa daya.

Za a yi wasan ne na ranar Talata a gidan Arsenal wato Emirates.