EL Clasico: Real Madrid da Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid da Barcelona suna da maki 18 kowannansu bayan buga wasannin mako na 8 a gasar La Liga

A cikin watan Nuwamba ne za a kara tsakanin Real Madrid da Barcelona a gasar cin kofin La Ligar Spaniya a wasan mako na 14.

Karawar da ake yi wa taken El Clasico za a fara wasan farko a filin Santiago Bernabeu a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburi da maki 18, yayin da Barcelona ma ke da maki 18 a matsayi na uku bayan da aka kammala buga wasanni takwas a gasar ta La Liga.

A karshen mako Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan Real Madrid da ya fi ci mata kwallaye, bayan da ya zura daya a karawar da suka doke Levente 3-0 a wasan La Liga a ranar Asabar.

Hakan ne ya sa Ronaldo mai shekaru 30, ya ci kwallo ta 324 daga wasanni 310 da ya yi wa Real Madrid.

Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi, wanda ke yin jinya, bayan da ya ji rauni a karawar da suka doke Las Palmas 2-1 a gasar La Liga, zai buga karawa da Real Madrid din.