Za a cigaba da Firimiyar Nigeria ranar Laraba

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Saura wasanni biyar a kammala gasar Firimiyar bana

Hukumar gudanar da gasar cin kofin firimiyar Nigeria, ta tsayar da ranar Laraba domin cigaba da buga wasannin mako na 34 na gasar.

A ranar Lahadi ya kamata a buga wasannin mako na 34, amma sakamakon karawa da Nigeria ta yi da Burkina Faso ya sa aka dage wasannin.

Nigeria ta ci Burkina Faso 2-0 a Fatakwal a ranar Asabar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta 'yan wasan da ke taka leda a gida.

Burkina Faso za ta karbi bakunci Nigeria a wasa na biyu a ranar 25 ga watan Oktoba a Ouagadougou.

Haka kuma hukumar ta dage karawa tsakanin Sunshine Stars da Rangers a ranar Larabar, sakamakon 'yan wasan Sunshine Shida suna tare da tawagar kwallon kafar Nigeria.

Gajerin wasanni mako na 34 da za a buga:

  • El-Kanemi v Giwa FC
  • Wikki v FC Ifeanyiubah
  • Heartland v Sharks
  • Shooting Stars v FC Taraba
  • Nasarawa Utd v Enyimba
  • Kwara Utd v Bayelsa Utd
  • Abia Warriors v Lobi Stars
  • Wolves v Akwa Utd
  • Sunshine Stars v Rangers
  • Dolphins v Kano Pillars