"Guardiola zai ci gaba da zama a Bayern Munich"

Image caption Bayern Munch za ta kara da Arsenal a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata

Bayern Munich ta ce tana da tabbacin cewar Pep Guardiola zai sabunta zamansa a matsayin mai horas da kungiyar kafin karshen kakar wasan bana.

Ana rade-radin cewar Guardiola dan kasar Spaniya, zai koma horas da Manchester City, kuma a cikin watan Satumba kocin ya fice daga dakin taro da 'yan jarida bayan da aka tambaye shi gaskiyar labarin.

Shugaban Munich din Karl Heinz Rummenigge ya ce "Hakika ana zawaracin kociyan, amma muna da tabbacin cewar Guardiola zai ci gaba da zama a Bayern".

Guardiola tsohon kociyan Barcelona ya koma Bayern ne a 2013, ya kuma jagoranci kungiyar ta lashe kofunan Bundesliga biyu.

A baya can kocin ya taba cewar idan har an samu wanda ya fi shi dace wa dai zai iya jan ragamar Munich, to a shirye yake ya ba shi dama.