Emenike ya yi ritaya daga Super Eagles

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Emenike ya kwashe shekru biyar yana murza leda a Super Eagles.

Dan wasan Super Eagles, Emmanuel Emenike, ya yi ritaya daga bugawa kungiyar kwallo bayan ya kwashe shekaru biyar a kulob din.

Sanarwar da dan wasan ya fitar a shafinsa na Instagram ranar Litinin ta ce, "Ba zan sake bugawa Eagles wasa ba! Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na daina buga wa kungiyar wasa bayan kwashe shekaru biyar domin a samu zaman lafiya."

Emenike ya godewa masu goyon bayan sa, yana mai cewa yana alfahari da kalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake taka leda a kungiyar.

Emenike ya buga wasanni 35 a Super Eagles, kuma ya zura kwallaye 16.