Ya kamata Falcao ya kara kaimi - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A farkon kakar wasan bana Falcao ya koma wasa aro Chelsea

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce ya kamata Radamel Falcao ya kara zage damtse fiye da Diago Costa idan har yana son a dinga saka shi a wasa akai-akai

Tun lokacin da Falcao ya koma wasa aro a Chelsea a watan Yuli, sau daya aka fara sa shi a wasan Premier da League Cup a Chelsea.

Dan wasan dan kasar Colombia, mai shekaru 29 ba zai kuma buga wa Chelsea wasan gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Dynnamo Kiev a Ukraine a ranar Talata ba.

Mourinho ya ce "Na fi son zabar dan kwallon da ya fi kwazo, kuma ya kamata ya kara kaimi fiye da Diego, domin da shi kawai muka dogara".

Haka kuma kocin ya karyata jita-jitar cewar Falcao dan wasan Monaco zai bar Stamford Bridge a watan Janairu.