U17: Nigeria ta lallasa Chile

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nigeria ce ta lashe gasar da aka yi a baya

Tawagar Golden Eaglets ta Nigeria ta kai zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa mai masaukin baki Chile da ci biyar da daya.

Samuel Chukwueze da Victor Osimhen sun ci kwallaye biyu kowannensu a yayin da Kelechi Nwakali shi ma ya zura kwallo daya.

Marcelo Allende ne ya farke wa Chile kwallo daya.

Nigeria ta tsallake zuwa zagaye na gaba tare da Koriya ta Kudu a yayin da Chile za ta hadu da Amurka a ranar Juma'a domin daya daga cikinsu ta tsallake zuwa mataki na gaba.