Dolphins ta doke Kano Pillars 2-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Saura wasanni hudu a kammala gasar Premier bana

Dolphins ta doke Kano Pillars da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 34 da suka kara a garin Fatakwal a ranar Laraba.

Adamu Hassan ne ya fara ci wa Pillars kwallo a minti na 17 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Dolphins ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Godbless Asamoah saura minti 26 a tashi daga karawar, sannan ya kara ta biyu daf da za a tashi daga wasan.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Wikki Tourist ta ci Ifeanyiubah 2-1, Heartland ta doke Sharks da ci daya mai ban haushi.

Nasarawa United da Enyimba tashi wasa suka yi canjaras babu ci, Giwa FC ta ci EL-Kanemi Warriors 2-1 har gida, sai Kwara United da Bayelsa United da suka tashi kunnen doki.

Ga sakamakon wasannin mako na 34 da aka yi:

El-Kanemi 1-2 Giwa FC Wikki 2-1 FC Ifeanyiubah Heartland 1-0 Sharks Shooting Stars 1-0 FC Taraba Nasarawa Utd 0-0 Enyimba Kwara Utd 1-1 Bayelsa Utd Abia Warriors 2-0 Lobi