Na kadu da jin ritayar Emenike - Oliseh

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oliseh ya ce zai so ya ji daga bakin Emeniki cewar ya yi ritaya

Kociyan tawagar kwallon kafar Nigeria, Sunday Oliseh ya ce ya kadu da ya ji cewar Emmanuel Emeniki ya yi ritaya daga buga wa Super Eagles tamaula.

Oliseh ya ce ya yi takaici da jin Emenike ya yi ritaya, sai dai kuma ya kara da cewar ba wanda ba za a iya maye gurbinsa ba. Ranar Litinin Emenike ya sanar da yin ritaya ta kafar sada zumunta ta Instagram.

Kocin ya kara da cewar har yanzu bai yarda da yin ritayar dan kwallon ba, domin har yanzu bai ji komai daga gareshi ba.

Kocin ya kuma ce Emenike yana daga cikin 'yan wasan da suke sawun gaba a tawagar Super Eagles da yake son yin amfani da shi.

Oliseh ya ce yana ta kokarin kiran dan wasan ta wayar sadarwa domin ya ji daga bakin sa, amma har yanzu hakansa ba ta cimma ruwa ba.