Mun samu kwarin gwiwa - Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abubuwa sun soma yi wa Wenger kyau

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce nasarar da suka samu a kan Bayern Munich ta kara musu kwarin gwiwa a gasar zakarun Turai.

Arsenal ta doke Bayern da ci biyu da nema a wasan da suka fafata a filin Emirates.

"Muna bukatar nasarar kuma mun matsa kaimi sannan muka samu sakamako," in ji Wenger.

Olivier Giroud da kuma Mesut Ozil ne suka ci wa Gunners din kwallayen biyu.

Arsenal za ta yi bugu na biyu tsakaninta da Bayern a birnin Munich a ranar 4 ga watan Nuwamba.

Bayern ta samu galaba a wasanni 12 a jere kafin rashin nasararta a hannun Arsenal.

  • BATE Bor 0-2 Barcelona
  • Bayer Levkn 4-4 Roma
  • Arsenal 2-0 Bayern Mun
  • Dinamo Zagreb 0-1 Olympiakos
  • Dynamo Kiev 0-0 Chelsea
  • FC Porto 2-0 Maccabi Tel Aviv
  • Valencia 2-1 KAA Gent
  • Zenit St P 3-1 Lyon