An kai Man City kara kan yi wa UEFA ihu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ko a bara ma wani gungun magoya bayan city sun wata zanga-zangar kin jinin hukumar.

An yi karar kulob din Manchester City gaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, bayan da aka ji magoya bayanta na ihun kin jinin taken gasar zakarun Turai a wasan da ya ci nasarar ci 2-1 da ta samu kan Sevilla ranar Laraba.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Iceland wanda ya sa ido kan wasan ne ya shigar da karar kuma yanzu an soma bincike domin daukar matakan ladabatarwa; inda za a saurari karar a watan Nuwamba.

An fahimci cewa kulob din Manchester City ba zai yi magana kan batun ba a halin yanzu, sai dai ana sa ran kungiyar ta kare magoya bayan nata a yayin sauraren karar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da magoya bayan City suka nuna fushinsu da hukumar ta UEFA ba.

Karin bayani