Za mu taka rawa a kofin zakarun Turai - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption A ranar Lahadi Manchester United za ta kara da Manchester City a gasar Premier

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya ce yana da tabbacin cewar zai kai zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai, duk da tashi 1-1 da suka yi da CSKA Moscow.

United tana mataki na biyu a kan teburi a rukuni na biyu da maki hudu, za kuma ta karbi bakuncin CSKA da PSV Eindhoven kafin ta ziyarci Wolfsburg a Jamus.

Van Gaal ya ce United tana yin kokari a wasannin da take yi a gida, saboda haka za ta lashe karawar da za ta yi, sannan ta kuma kai wasannin zagaye na biyu a gasar.

CSKA ce fara cin United kwallo a raga ta hannun Seydou Doumbia, daga baya ta farke kwallon ta hannun Anthony Martial a karawar da suka yi a ranar Laraba.