An kai wa magoya bayan Tottenham hari

Image caption Sion Roberts daya daga cikin wadanda hari ya rutsa da su ne ya saka wannan hoton a shafin Twitter.

An kai wa wata tawagar magoya bayan Tottenham hari a birnin Brussels kafin wasan kulob din da Anderlecht a gasar Europa League.

Ganau sun ce kimanin magoya bayan Tottenham 50 ne ke hutawa a cikin wani gidan abinci a babban birnin na kasar Belguim ranar Laraba lokacin da kusan mutane 100 suka yi kokarin afkawa ciki.

Wata ma'aikaciyar shagon Marie Elizabeth ta shaida wa BBC cewa shigar mutanen ke da wuya sai suka fara duka mutane da kujeru da tebura da ma duk wani abin da suka samu.

An ce an ji wa mutum daya mummunan rauni a cikin harin.

Karin bayani