'Watakila Kompany ba zai buga wasa da United ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ranar Lahadi ne za a kara tsakanin Manchester United da Manchester City

Watakila Vincent Kompany ba zai buga karawar da Manchester City za ta yi da Manchester United a gasar Premier a ranar Lahadi ba in ji Manuel Pellegrini.

Manchester United ce za ta karbi bakuncin Manchester City a gasar cin kofin Premier a ranar Lahadi a Old Trafford.

City ta saka Kompany daf a tashi a wasa a fafatawar da ta doke Sevilla 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a ranar Laraba.

Nicolas Otamendi da Eliaquim Mangala ne suka buga wasa tare a ranar Laraban, kuma Pellegrini ya yaba da rawar da suka taka.

Kompany ya yi jinyar raunin da ya ji a karawar da City ta yi da Juventus a gasar zakarun Turai a ranar 15 ga watan Satumba a Ettihad.

Kuma dan kwalllon mai tsaron baya, bai buga wa City wasan Premier da ta yi da Bournemouth a ranar Asabar ba.