Zan iya yin kuka idan aka tafi hutu -Wenger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsene Wenger ya ce bai kamata a yada al'adar kasar Ingila da na kwallon kafa da ke cigaba da wasa duk da akwai hutun hunturu ba.

Manajan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce zai iya yin kuka idan har hukumar shirya gasar Premier ta kirkiro da hutun karshen shekara.

Kulob din sa dai na da wasanni 7 tsakanin ranakun 13 ga watan Disamba da 16 ga watan Janairu, ciki har da wasanni uku cikin kwanaki bakwai a watan Disamba.

''Buga wasanni a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara al'ada ce ta kasar Ingila da kuma ta kwallon kafa, kuma ni ina son in ci gaba da bin ta" In ji Wenger.

Amma manajan kulob din Manchester United, Louis van Gaal ya ce rashin bayar da hutun wasanni a karshen shekara a Ingila a zaman wata mummunar al'ada.

Su ma Manchester United suna da wasanni bakwai tsakanin ranakkun 13 ga watan Disamba da kuma 16 ga watan Junairun shekarar 2016, inda suke da wasannin uku jere a cikin kwanaki tara tsakanin ranakun 19 da 28 ga watan Disamba.