Sturridge ba zai buga wasa da Southampton ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daniel Sturridge na fama da rauni a gwiwarsa.

Dan wasan Liverpool Daniel Sturridge na nuna shakku game da yiwuwar taka leda a wasan da kulob din zai yi da Southampton ranar Lahadi, domin kuwa za a dauki hoton gwiwarsa.

Sturridge, mai shekaru 26, bai buga wasanni biyu da kulob din ya yi ba sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa a lokacin da yake yin atisaye gabanin kunnen-dokin da suka yi da Tottenham a gasar Premier.

Da aka tambayi kociyan Liverpool Jurgen Klopp ko akwai yiwuwar Sturridge ya buga wasa ranar Lahadi, sai ya ce: "Muna samun ci gaba a kowacce rana. Idan dai zai iya yin atisaye ba tare da matsala ba, to yana da zabi."

Christian Benteke da Roberto Firmino na sa ran buga wasa bayan sun kammala jinyar da suka yi.

Benteke ya yi jinyar wata guda, yayin da Firmino ya dawo daga ciwon bayan da ya yi.

Sturridge ya zura kwallaye 24 a wasanni 33 da ya buga a kulob din a kakar wasa ta 2013-14 inda Liverpool ya zo na biyu a saman tebur, sai dai ya sha fama da raunuka a kwanakin nan.