Fifa: Jerome Champagne zai tsaya takara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Champagne ya ce zai rika wallafa albashin shugabannin Fifa.

Tsohon mai bai wa shugaban Fifa Sepp Blatter shawara, Jerome Champagne, ya ce zai tsaya takarar shugabancin hukumar.

Champagne ya yi yunkurin fafatawa da Blatter a zaben da aka yi a watan Mayun da ya gabata, sai dai bai samu goyon bayan da yake bukata domin yin takara ba.

Dakatarwar da aka yi wa Blatter da shugaban Uefa Michel Platini daga harkokin wasa a kan zargin cin hanci ta sanya wa Champagne kaimin tsayawa takarar shugabancin hukumar.

Ya sha alwashin wallafa albashin da shugabannin hukumar ke dauka a jaridu domin gudun zargin aikata ba daidai ba.

Sanarwar tasa ta tsayawa takara na zuwa ne gabanin wa'adin da aka dibarwa duk mai son tsayawa takara ya bayyana sha'awarsa ta yi hakan kafin ranar Litinin.

Za a gudanar da zaben shugabancin Fifa ne ranar 26 ga watan Fabrairu mai zuwa.