Arsenal ta dare mataki na daya a teburin Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal ta yi wasanni 10 tana da maki 22 kuma ta daya a kan teburi

Arsenal ta koma mataki na daya a kan teburin Premier bayan da ta ci Everton 2-1 a wasan gasar Premier da suka yi a Emirates a ranar Asabar.

Arsenal ta ci kwallon farko ta hannun Olivier Giroud, sannan Laurent Koscielny ya kara ta biyu a raga.

Everton ta farke kwallo daya ta hannun Ross Barkley, kuma Rumelu Lukaku ya samu damar farke kwallo ta biyu, amma da ya buga ta bugi turke.

Everton ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili bayan da aka bai wa Gareth Barry jan kati daf da za a tashi daga fafatawar.

Rabon da Arsenal ta hau kan teburin Premier tun a cikin watan Fabrairu, kuma sai a ranar Lahadi ne Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a Old Trafford.

Ga sauran wasannin Premier da za a buga a ranar Lahadi:

  • Sunderland v Newcastle
  • Bournemouth v Tottenham
  • Man Utd v Man City
  • Liverpool v Southampton