Real Madrid ta yi wasanni 12 ba a doke ta ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Madrid ta bai wa Celta Vigo wacce ke matsayi na biyu a kan teburi tazarar maki uku

Real Madrid ta yi wasan na 12 ba a doke ta ba a bana, bayan da ci Celta Vigo 3-1 a gasar La Liga wasan mako na tara da suka kara a ranar Asabar.

Cristiano Ronaldo ne ya fara cin kwallo a minti na takwas da fara tamaula, kuma kwallo ta 12 da ya ci wa Real Madrid tun fara kakar wasannin bana.

Madrid ta kara ta biyu a raga ta hannun Danilo dan Brazil, daga nan ne kuma aka kori dan wasan Celta daga fili Gustavo Cabral a minti na 57.

Celta ta zare kwallo daya ta hannun Nolito, kuma daf da za a tashi wasa Mercelo ya ci wa Madrid kwallo ta uku a raga.

Madrid ta fara yin canjaras da Sportin Gijon a cikin watan Agusta, daga nan ne ta lashe wasanni bakwai ta kuma yi canjaras a fafatawa uku.

Real Madrid din tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 21.

Ga wasannin La Liga da za a buga a ranar Lahadi:

  • Levante vs Real Sociedad
  • Las Palmas vs Villarreal
  • Barcelona vs Eibar
  • Atl├ętico Madrid vs Valencia