Mourinho ya ki yin magana da 'yan jaridu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau biyar ana doke Chelsea a gasar Premier bana

Jose Mourinho bai yi hira da 'yan jaridu ba, bayan da aka tashi wasan da West Ham ta doke su da ci 2-1 a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar.

A kuma karawar ne alkalin wasa Jonathan Moss ya kori Mourinho daga wasan a inda ya umarce shi da ya koma cikin 'yan kallo.

Tun a ranar Juma'a Mourinho ya gargadi 'yan jaridu da cewar zai sauya mu'amala da su bayan da aka dauki hotonsa a kamara a Arewacin Landan aka kuma wallafa a jaridu.

Bayan da Mourinho ya ki tattaunawa da 'yan jaridun ne Garry Cahill ya yi magana da su a inda ya ce suna cikin takaici a wasannin da suke yi.

Mouro Zarate ne ya fara cin Chelsea a karawar, kafin daga baya Gary Cahill ya farke kwallo, kuma Andy Carroll ya ci wa West Ham ta biyu daf da za a tashi daga fafatawar.

Doke Chelsea da aka yi a wasan shi ne karo na biyar da ta yi rashin nasara a wasanni 10 da ta buga a gasar Premier bana.

Haka kuma a karawar ce aka bai wa kociyan Chelsea Mourinho jan kati da mataimakinsa Silvino Louro da kuma dan wasansa Nemanja Matic.