Man United da Man City sun tashi Canjaras

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana mataki na hudu a kan teburi, City tana matsayi na daya

Manchester United ta buga canjaras da Manchester City a wasan hamayya da suka buga a filin wasa Old Trafford a ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun faffata kafin aje hutun rabin lokaci, kuma sai da aka dawo daga hutu ne suka zafafa kai hare-hare.

Jesus Navas ya samu dama a inda ya buga kwallo ta nufi ragar United sai dai David De Gea ya yi mata gada saura minti takwas a tashi daga karawar.

Kuma ba a dauki lokaci ba United ta samu dama ta hannun Jesse Lingard wanda ya buga kwallon ta bugi turke daga bugun da Anthony Martial ya yi yo masa.

Da wannan sakamakon Manchester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier da maki 22.

Manchester United kuwa ta koma matsayi na hudu a kan teburin da maki 20 dai-dai da na West Ham wacce take mataki na uku a teburin.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

  • Sunderland 3 - 0 Newcastle
  • Bournemouth 1 - 5 Tottenham