Nigeria ta samu tikitin shiga gasar nahiyar Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rwanda ce za ta karbi bakuncin wasannin cin kofin Afirka da za a yi a bana

Burkina Faso da Nigeria sun tashi canjaras a wasa na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara a Ouagadougou a ranar Lahadi.

A wasan farko da suka buga a mako biyu da suka wuce Super Eagles ce ta ci Etalons 2-0 a karawar da suka yi a Fatakwal.

Da wannan sakamakon Nigeria ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasa da suke taka leda a gida da za a yi a Rwanda a shekara mai zuwa.

Wasu kasashen da tuni suka sami damar shiga gasar sun hada da mai masaukin baki Rwanda da Morocco da Tunisia da Angola da Gabon da Mali da Guinea da kuma Jamhuriyar Congo.

Sai a ranar juma'a ne Ivory Coast za ta fafata da Ghana a wasa na biyu da za su yi Abidjan, a wasan farko da suka yi a filin wasa na Baba Yara, Ghana ce ta ci Ivory Coast 2-1.