An bai wa Super Eagles karin ladan wasanni

Hakkin mallakar hoto TheNFFTwitter
Image caption Rwanda ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka na 'yan wasan dake taka leda a gida

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta saka wa tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta 'yan wasa da ke taka leda da kudade, bisa gurbin da ta samu na shiga gasar cin kofin Afirka.

A ranar Lahadi ce Nigeria ta buga canjaras da Burkina Faso a Ouagadougou, kuma makonni biyu da suka wuce Super Eagles ce ta ci Etolens 2-0 a Fatakwal.

NFF ta ce a bai wa kowane dan wasa na Super Eagles dala dubu daya ladan samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka leda a gida, da za a yi a shekara mai zuwa a Rwanda.

Kawo yanzu kasashen da suka samu damar shiga gasar sun hada da mai masaukin baki Rwanda da Morocco da Tunisia da Angola da Zambia da Uganda da Ethiopia da Mali da Guinea da Gabon da Jamhuriyar Congo da Niger da kuma Zimbabwe.

Sauran gurabai biyu da suka rage shi ne wadanda za a fafata tsakanin Ivory Coast da Ghana da kuma wasan Kamaru da Congo Brazaville.