Song ya zama kociyan Chadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Song bashi da kwarewa a kan horas da kwallon kafa

Hukumar kwallon kafa ta Chadi ta dauki tsohon dan wasan kwallon kafar Kamaru, Rigobert Song a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafar kasar.

Song mai shekaru 39, ya maye gurbin Emmanuel Tregoat wanda kwantiraginsa da Chadi ya kare a ranar 30 ga watan Satumba.

Kociyan zai fara jan ragamar tawagar kwallon Chadi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2018 da za su fafata da Masar a cikin watan Nuwamba.

Chadi ce za ta fara karbar bakuncin Masar a wasan farko da za su fara karawa a ranar 14 ga watan Nuwamba a N'Djamena.

Song ya bugawa tawagar kwallon kafa ta Kamaru wasanni sama da 100 kafin ya yi ritaya, kuma shi ne dan Afirka na farko da ya je gasar cin kofin duniya sau hudu.