Mutane bakwai na takarar shugabancin Fifa

Hakkin mallakar hoto Fifa
Image caption A watan Fabarairu badi za a yi zaben

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce mutane bakwai ne ke tarakar kujerar shugabancinta.

'Yan takarar su ne: shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya, Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa da Yarima Ali bin al-Hussein na Jordan da kuma shugaban hukumar kwallon Liberia Musa Bility.

Sauran su ne Jerome Champagne da Gianni Infantino da shugaban Uefa da aka dakatar Michel Platini, da kuma dan kasar Afrika ta Kudu Tokyo Sexwale.

Shugaban Fifa na yanzu, Sepp Blatter an dakatar da shi na tsawon kwanaki 90 bisa zargin cin hanci da rashawa.

Shi ma Platini an dakatar da shi amma kuma Fifa ta ce za a barshi ya yi takara idan har wa'adin dakatarwar ta kare.

Blatter da Platini sun musanta zargin cin hanci da rashawa da ake musu.